24 Faburairu 2020 - 05:10
​Yemen: Shekarar 2020 Shekara Ce Ta Kare Sararin Samaniyar Kasa

Ma’aikatar tsaron kasar Yemen ta ce a cikin shekara ta 2020 za ta fara yin amfani da wasu sabbin makamai na musamman domin kare sararin samaniyar kasar daga hare-haren masu yin shishigin a kan kasar.

(ABNA24.com) Ma’aikatar tsaron kasar Yemen ta ce a cikin shekara ta 2020 za ta fara yin amfani da wasu sabbin makamai na musamman domin kare sararin samaniyar kasar daga hare-haren masu yin shishigin a kan kasar.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, ministan tsaro na gwamnatin san’a Brigadier janar Muhammad Nasir Alatifi ya bayyana cewa, lokaci ya wuce da sararin samaniyar kasar zai ci gaba da kasancewa wurin shawagin jiragen yakin kasashe masu kisan mata da kananan yara.

Ya ce a yau an kaddamar da sabbin makamai masu linzami na kariya wadanda za su shiga aiki, kuma daga yanzu za su rika harbo jiragen yakin ba tare da wata tantama ma.

A cikin wannan makon ne jiragen yakin Saudiyya suka yi luguden wuta a kan gidajen jama’a alardin jauf na kasar ta Yemen, inda suka kashe fararen hula 31 akasarinsu mata da kananan yara, wanda hakan yasa dakaruin na Yemen suka mayar da martani da makamai masu linzami a kan babban kamfanin main a masarautar iyalan gidan Saud.



/129